Rundunar sojin sama ta Najeriya karbi wani sabon jirgin yaki kirar ATR-42 da za ta rika amfani dashi wajen leken asiri tare da kaddamar da hare-hare kan ‘yan ta’adda.

Mai Magana da yawun rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce hakan na daga cikin shirye-shiryen da rundunar take dashi na kara kaimi a yaki da take da ayyukan ta’addanci tare da tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Daramola ya ce fiye da shekaru 5 da suka gabata, rundunar sojin sama tare da hadin gwiwar wasu bangarori na aiki tukuru domin fito da wasu sabbin dabarun kayan yaki.

Ya ce shirye-shiryen da aka yin a kasar Jamus, ya taimakawa rundunar a bangaren kere-kere da musamman jami’an sojin da suka halarci taron da kansu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *