Gwamnatin jihar Yobe ta ce tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da malaman addinin Musulunci domin zamanantar da harkokin almajiranci a fadin jihar.

Kwamitin da Gwamnan jihar Mai Mala Buni ya kafa domin yi wa almajiranci kwaskwarima ya ce yana tuntubar wadanda ya kamata domin tabbatar da an ba kowa hakkinsa.

Matakin na gwamnatin jihar na zuwa ne yayin da wasu jihohi ke kokarin soke shirin almajirancin tare da hana yaran zuwa wasu jihohi ko garuruwa da sunan neman ilimi.

Shugaban kwamitin da gwamnan na Yobe ya kafa Muhammad Sani Idris, ya ce sun gana da shahararren malamin addinin Musuluncin nan da Sheikh Dahiru Usman Bauchi inda suka yi masa bayanin kudurce-kudurcen gwamnatin Yobe.

A cewarsa, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi maraba da batun inda ya bayyana musu cewa hakan shi ne zai kawo ci gaban al’amuran kasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *