Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin da zai bada shawarwari kan mamtakan da za a dauka na gaba akan yaran da aka sace a jihar.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya kaddamar da kwamitin domin a Kano.

Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai, ya ce Ganduje ya naɗa mai shari’a Wada Abubakar Umar Rano a matsayin shugaban kwamitin.

Ya ce mutanen da su ka gabatar da rahoton bincike game da sace yaran su ne aka kara nadawa a cikin kwamitin domin zartar da abubuwan da su ka zayyana.

A cikin shawarwarin da kwamitin binciken da aka kafa a watan Oktoba na shekara ta 2019 ra rubuta, ya bayyana yadda za a iya nemo sauran yaran da ake zargin har yanzu ba a kai ga ganowa ba.

Da ya ke kaddamar da kwamitin, Ganduje ya ce matukar laifuffuka su na karuwa aikin kwamitin zai ci gaba da karuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *