Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawallen Maradun, ya ce ba ya nadamar matakin da ya dauka na yin sulhu da ‘yan bindigar da su ka addabi jihar sa.

Matawalle ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Zailani Bappa ya fitar, inda ya ce sulhun shi ne hanyar da ta fi dacewa wajen kawo karshen hare-haren da ‘yan bindigar su ka kwashe tsawon shekara da shekaru su na kaiwa a jihar da ma wasu jihohin arewa.

Ya ce sun yi tattaunawar zaman lafiyar ne a matsayin hanyar gaskiya ta magance matsalolin jihar Zamfara, kuma sun samu ci-gaban da ba a yi tsammani ba a shekara daya da ta gabata.

Sai dai ya ce dole dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar su kasance masu gaskiya idan ana son dorewar zaman lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *