‘Yan ta’addan Boko Boko Haram sun kai hari kan ɗaya daga cikin jiragenta masu saukar ungulu a yankin Damasak na jihar Borno.

Shugaban sashin jinƙai na hukumar da ke Najeriya Edward Kallon ya bayyana haka a shafinsa na twitter.

Ya ce harsasai da ‘yan ta’addan suka yi amfani dasu wajen harbin jirgin sun lalata shi kuma ya tsayar da ayyukan jinƙai da ake yi a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

Majalisar dai ta yi Allah wadai da harin da ƙungiyar ta kai, sannan ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gudanar bincike kan harin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *