Rundunar tsaro ta Civil Deffence a Kaduna, ta kama wani Faston Cocin Faith Agape da ke Narayi mai suna Joseph Alhassan, bisa laifin lalata da ‘yar aikin sa na tsawon shekaru biyar.

Iyayen yarinyar, ‘yar asalin karamar hukumar Kagarko sun tafi da ita bayan samun labarin abin da ya faru tsakanin ta da faston.

Sai dai Faston, wanda dan Asalin Karamar hukumar Lere ne ya karyata zargin da ake masa.

Tuni dai ma’aikatar kula da walwalar al’umma ta jihar  Kaduna ta shigar da kara kotu, ta na tuhumar Faston.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *