Ministan sadarwa da fasahar zamani Isa Ali Pantami, ya ce albashin da alawus-alawus da yake samu a matsayinsa na minista bai kai wadanda yake samu a baya ba a matsayin Farfesa a jami’ar Madina.

Pantami na maida martini ne akan rahotanni dake yawo a kafofin sadarwa cewa ya mallaki wasu manyan gidaje guda 3 a babban birnin tarayya Abuja bayan hawansa kujerar minista shekarar da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Pantami ya ce ya amsa kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kawai saboda ya dawo gida Najeriya ya bada gudunmawa domin ciyar da kasar gaba.

Sanarwar ta ce ministan bai mallaki wani gida ko fili a ko ina ba, tun bayan hawansa kan karagar mulki.

Ta kara da cewa daya daga cikin gidajen da aka gani a hoton Pantami ya siya ne tun watan Janairun 2017, sama da shekaru 2 kafin ya zaman minister, ya yin da daya kuma a cikin hoton gidan da ya kama haya ne a watan disambar shekarar da ta gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *