Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an sake samun mutane 454 da suka kamu da cutar Korona a gwaje-gwajen da aka yi cikin awa 24.
Hukumar wacce ta bayyana haka a shafin ta na twitter, ta kara da cewa mutane 12 suk sake mutuwa sakamakon kamuwa da cutar a cikin wannan lokaci.
Adadi mafi yawa na masu korona da aka sake samu, ya fito ne daga Lagos, jihar da cutar ta fi ƙamari tun bayan bullarta a Najeriya, inda yanzu yawan masu korona a jihar ya kusa kai dubu 11.
A jihar Kaduna ma an sake samun mutane 17 da suka kamu da cutar ta korona.
Cutar ta bulla a Najeriya ne a ranar 27 ga watan Fabrairu bayan wani bature dan kasar Italiya ya shigo ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *