Gwamnatin jihar Kaduna ta kammala kashin farko na aikin kasuwan Zamani da ta ke ginawa a Kasuwar Magani dake karamar hukumar Kajuru.

Mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Ibrahim Musa, ne bayyana haka a lokacin da ya jagoranci tawagar manema labarai zuwa kasuwar.

Ya ce aikin kasuwar da ya ci naira billiyan 2 mai shaguna da dama ya kusa kammaluwa.

Ya ce an kammala shaguna dari 4 daga cikin kashin farko na aikin, wanda hakan ke tabbatar da cewa an kammala kashi 80 cikin dari na aikin kasuwar.

Idan dai za a iya tunawa gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ne ya kaddamar da aikin da zummar inganta harkokin tattalinj arziki da cinikayya a tsakanin al’ummomin jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *