Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kama sama da mutane 14 bisa zargin aikata laifukkan ta’addanci daban-daban a fadin jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Kaoje, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan irin nasarorin da rundunar ta samu a ‘yan kwanakin nan.

Ya ce rundunar ta kama Halima Mohammed, Mamman Mohammed, Ibrahim Muhammad, Abubakar Muntari, Chiso Yaro, da kuma Sa’adu Sanusi bisa laifukkan fashi da makami, tsafece-tsaface, luwadi, madigo da sauransu.

Ya ce ire-iren wadannan laifukka ke sanya al’ummomi da basu ji ba basu gani ba, cikin halin matsi da kunci na rayuwa, wanda a cewarsa rundunar ba za ta yi sakwa-sakwa wajen hukunta duk wanda aka kama ba.

Kwamishinan ya kara da cewa a ranar 25 ga watan Yuni, rundunar ta kama wasu da suka hada da Abdullahi Ibrahim da Tukur Ibrahim da suka fito daga kauyen Tungar Rana a karamar hukumar Kware dake jihar kan yunkurin yin fashi da makami.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *