Rundunar soji ta musamman dake yaki da ayyukan Boko Haram da aka yi wa lakabi da Operation Lafiya Dole ta lalata wurin ganawar ‘yan ta’addan Boko Haram dake Mainyakare dake kusa da kusa da Sambisa a jihar Borno.

Babban jami’in kula da sashen yada labarai da hulda da jama’a na shelkwatar tsaro Majo Janar John Enenche, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce jami’an sojin sun kara da kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan a  harin da suka kai musu.

Enenche ya ce harin da jami’an sojin suka kai ta sama ya zo ne sakamakon bayanan sirri da suka samu na cewa ‘yan ta’addan na Boko Haram na amfani da wani katafaren gini dake yankin a matsayin wajen ganawa.

Ya ce samun labarin ke da wuya rundunar sojin ta tashi jiragen yakin sojin sama inda suka kai harin a lokacin da ‘yan ta’addan ke zama, inda nan take jirgin farko ya kai hari daidai inda ‘yan ta’addan suka taru.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *