Shelkwatar tsaro ta Najeriya ta ce jami’an sojin sun lalata wasu matatun man fetur tare da kama wasu barayin mai a wasu aikace-aikacen da suka gudanar a yankin kudu maso kudancin kasar nan.

Babban jami’in yada labarai da hulda da jama’a John Enenche, ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi kan aikace-aikacen rundunar a cikin makwanni 2 da suka gabata. 

Ya ce daga ranar 18 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli rundunar sojin tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun samu gaggarumar nasara a yankin na Kudu maso kudancin Najeriya.

Enenche ya ce kokarin da jami’an tsaron suka yi ya kai ga kwato buhunan shinkafa ‘yan kasashen ketare 135, da kuma wani kwale-kwale da ake amfani dashi wajen yin fasa kwabri.

A cewarsa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da hada hannu da sauran hukumomin tsaro wajen yaki da ayyukan ta’addanci, samar da tsaro da kuma zaman lafiya.

Sannan ya yabawa kokarin na jami’an soji da sauran jami’an tsaro da suka bada gudunmawa wajen cin nasara a hare-haren da suka kai a yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *