Gwamnatin tarayya ta ce ta shirya kara karfafa dangantaka dake tsakaninta da kasar Indonesia kan harkokin aikace-aikacen jami’an soji na yaki da ta’addanci.

Ministan tsaro Bashir Magashi, ya sanar da haka a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar ta Indonesia a Najeriya Usra Harahap, a ofishinsa dake Abuja.

Magashi ya ce babban makasudin ziyarar da jakadan ya kai masa shine domin kara karfafa dankon dangantaka dake tsakanin kasarsa da Najeriya wanda aka kafa tun 1965.

Ya ce tawagar ta mutane 4 ta gana da babban sakataren ma’aikatar tsaro Sabiu Zakari, da sashen hadakar bangarori Olu Mustapha.

Ministan ya kara da cewa kasashen biyu za su yi kokarin fito da sabbin dabaru da jami’an soji za su yi amfani dasu wajen inganta harkokin tsaro a kasashen biyu.

A nasa jawabin jakadan na Indonesia a Najeriya ya yabawa ministan tsaron bisa yadda yake jagorantar hukumomin tsaron Najeriya cikin tsari, yin abubuwan da zai sa jami’an tsaron amfani da kwarewarsu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *