Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an sake gano masu dauke da cutar korona 626 a gwaje-gwajen da aka gudanar cikin kwana guda.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na twitter, wannan na zuwa ne kwana guda bayan samun adadi mafi yawa na masu cutar a kwana guda tun bayan ɓullarta Najeriya.

A cewar hukumar, yanzu yawan mutanen da annobar korona ta kama a Najeriya ya kai dubu 27 da dari da 10.

Hukumar ta ce mutane 13 cutar ta kashe a ranar Alhamis din nan, inda adadin wadanda suka rasa rayukansu ya karu zuwa 616, tun bayan bullar ta.

A ranar Laraba 2 ga watan Yuli ne, aka samu adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar a kwana guda inda aka samu mutane 790.

Cutar Korona ta bulla a Najeriya ne ranar 27 ga watan Fabrairu a jikin wani bature dan kasar Italiya, bayan ya shigo ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *