Gwamnatin tarayya ta samar da kilogram dubu 38 da dari da 42 na sabon irin shuka na Kashu ga manoman jihar Kogi.

Ministan kula da harkokin noma da raya karkara Sabo Nanono, ya sanar da haka a lokacin da yake gabatarwa manoman jihar sabbin tsare-tsare da aka shigo dasu a Lokoja.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta dau wannan matakin ne domin dakile irin barazanar da cutar korona ke yiwa bangaren aikin gona a Najeriya.

Ya ce ma’aikatar kula da harkokin noma da raya karkara tare da hadin gwiwar ma’aikatar kula da harkokin jin kai da ci gaban kasa ne suka shirya shirin.

Nanono ya kara da cewa akwai karin irin shuka na zamani da aka samar na waken soya, masara, shinkafa, alkama, cocoa, dankalin hausa da sauran su.

Ya ce za a rana irin shukan ne ta hanyar amfani da kungiyoyin manoma, kungiyoyin mata da na matasa da kuma kungiyoyin da aka kafa na al’umma domin tabbatar da cewa ba a samu matsalar karancin abinci a Najeriya ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *