Ma’aikatar kula da harkokin ilimi ta jihar Kaduna ta fito da wani sabon shirin koyar da karatun mako-mako ta hanyar amfani da kafafen radio da talabijin.

BabbaR sakatariya a ma’aikatar Phoebe Yayi, ta sanar da haka a Kaduna, ta ce shirin zai rika zuwa ne a kowacce ranar Laraba daga karfe 10 zuwa 11 na safe.

A cewarta akwai malamai da dama da za su rika koyar da darussa, sannan za a ba masu koyi damar kira ta wayar tarho domin su tambayi duk wani abu da basu gane ba.

Ta ce shirin ya samu goyon bayan babban bankin duniya, da hukumar hadakar ilimi ta duniya da kuma cibiyar habaka ilimi na Najeriya.

Ta ce shirin zai ba dalibai malamai da kuma iyaye da sauran masu ruwa da tsaki damar kira ta wayan tarho domin yin tambayoyi ko kuma bada gudunmawa.

Phoebe ta ce hukumomin da suka karawa shirin kwarin gwiwa sun kuma dau nauyin horar da malamai kan hanyoyin da za su yi amfani da yanar gizo, da kuma sauran fasahohin zamani da ake amfani dasu wajen ganawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *