Gwamnan jihar Bauchi a arewacin Najeriya Bala Muhammad, ya dakatar da Sarkin Misau, Ahmed Sulaiman biyo bayan rikicin da ya barke a yankin tsakanin manoma da makiyaya.

Gwamnan ya sanar da dakatar da Sarkin ne yayin ƙaddamar da wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rikici dake da alaka da wani fili a yankin.

Rikicin da ya auku a garin Zadawa da ke karamar hukumar ta Misau, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane tara da jikkata wasu da dama.

Gwamnan ya kuma dakatar da wasu sarakunan gargajiya masu mukaman Hakimai da dagatai a yankin da rikicin ya shafa.

Sarkin Misau dai na daga cikin manyan sarakunan gargajiya a jihar ta Bauchi.

Kafin dakatar da basaraken gwamnan ya dakatar da shugaban riko na karamar hukumar ta Misau da wasu manyan jami’an karamar hukumar, da ake zargi da yin sakaci da rikicin.

Gwamnan ya ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki har tsawon makwanni 3 da aka ba kwamitin da aka kafa ya gabatar da rahotonsa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *