‘Yan ta’adda sun sace mutane 30 bayan kashe jami’an tsaro biyu a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa.

Shugaban karamar hukumar, Muhammad Otto, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun kashe jami’an tsaron sa kan biyu ne a  lokacin da suka musu kwantan bauna a kusa da tsaunin Onda.

Ya ce an gudanar da jana’izar gawarwakin bayan an dawo da Nasarawa daga tsaunin.

Wata majiyar ta ce wasu yan ta’addan daban sun tare babbar hanyar zuwa Udege/Loko na tsawon awanni a ranar Litini din da ta gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *