Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci ministar kudi kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, domin bayani kan matakan dakile asarar kudaden shiga sakamakon rashin biyan haraji da sauran su.

Majalisar yayin zamanta, ta gayyaci ministar da sauran wasu jami’an dake kula da hukumomin hada-hadar kudi domin su bayyana a gaban kwamitin dake kula da harkokin kudi da kuma na yaki da cin hanci da rashawa.

Majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan kudirin da dan majalisa Gershom Bassey ya gabatar.

Bassey ya gabatar da wannan bukata ne domin a yi bita kan tsarin dakile haramtattun hanyoyin hada-hadar kudade tare da yi wa wadanda suka ki biyan haraji afuwa ba tare da an hukunta su ba.

Ya ce Najeriya ta yi asarar akalla dala biliyan 140 ta haramtattun hanyoyin hada-hadar kudade a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2014, musamman a harkar danyen man fetur.

Sauran wadanda majalisar ta gayyata sun hada da gwamnan babban bankin Najeriya; Godwin Emefiele, shugaban hukumar tara kudaden haraji na kasa, Muhammad Mamman Nami.

Sauran sun hada da mai rikon mukamin shugaban yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC; Ibrahim Magu, da Shugaban Hukumar da ke tattara bayanai a kan laifukan da suka shafi kudi da ta`addanci ta kasa NFIU, Modibbo Hamman-Tukur.

Sai kuma shugaban kamfanin man fetur a kasa NNPC, Mele Kolo Kyari, Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC; Bolaji Owasanoye da shugaban bankin NEXIM; Roberts U. Orya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *