Cutar korona ta yi sanadiyyar mutuwar kwamishinan lafiya na jihar Ondo Wahab Adegbenro.

Wani jami’in gwamnatin jihar ya tabbatar da mutuwar kwamishinan bayan rahotanni sun bayyana cewa ya rika shan magani dan kanshin kansa domin rabuwa da cutar.

Kwaminshinan ya mutu ne a asibiti gwamnatin tarayya dake Owo hakan yasan sauran makarabben gwamnatin jihar cikin fargaba bayan da dama daga cikin su sunyi mu’amala da mamacin.

Tuni dai gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya killace kansa bayan gwaji ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar ta korona a farkon makon nan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *