Kamfanin jiragen sama na Aero dake aiki a Najeriya ya ce za a killace duk fasinjan da ya yi atishawa a cikin jirgin kamfanin ko da kuwa lafiyarsa kalau.

Shugaban kamfanin Aero, Ado Sanusi bayyana haka a lokacin da yake magana a wata kafar talabijin, ya ce kamfanin ya tanadi wurin killacewa da jami’an kula da lafiya da za su kula da waɗanda aka ga alamomin cutar korona tattare dasu.

Ado ya shawarci matafiya waɗanda ba su da lafiya su zauna gida har sai sun samu lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *