Gwamnatin jihar Kano ta cire dokar takaita zirga-zirga da ta sanya a fadin jihar domin takaita yaduwar cutar korona.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ce ta sanar da hakan a shafinta na twitter.

Gwamnatin ta kuma umurci ma’aikata daga mataki na 12 zuwa sama su koma aiki daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli.

Gwamnatin jihar ta ce ana ci gaba da tattaunawa kan ranar da za a bude makarantu ga dalibai da ke shekarar karshe da masu rubuta jarrabawar kammala aji uku da ‘yan firamare masu rubuta jarabawar shiga sakandare.

Ta ce dukkanin al’ummomin jihar za su iya komawa gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, amma ya zama wajibi su rika daukar matakan kariya, kamar yadda hukumomin lafiya suka umarta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *