Jam’iyyar APC ta nada Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai jogoranci kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Edo.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da jam’iyyar ta fitar dauke da sa hannun mataimakin sakataren yada labarai na kasa Yekini Nabena.

Kwamitin da Ganduje mai kunshe da mutane 49 zai yi aike ne wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar.

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodima ne zai kasance mataimakin Ganduje, sai kuma Abbas Braimoh a matsayin sakataren kwamintin yakin neman zaben.

An kafa kwimitin ne bayan amincewar shugabanta na riko gwamanan jihar Yobe Mai Mala Buni a zaben da ake sa ran gudanarwa a ranar 19 ga watan Satumba 2020.

A ranar Litinin 6 ga watan Yuli, jam’iyyar za ta kaddamar da soma aikin kwamitin a babban birnin tarayya Abuja.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *