Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce ta miƙa dan Najeriyar nan da ake zargi da damfara, Raymond Igbalode Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, ga hukumar liken asiri ta FBI a Amurka.

Hukumar ‘yan sandan Dubai ne suka sanar da hakan a wani sako da suka wallafa a shafinsu na Twitter.

Jami’an ‘yan sandan sun kama wadanda ake zargin ne a wasu jerin samame da suka kai a Dubai, inda suka katse shirin ‘yan damfarar na karbar makudan kudade daga hannun jama’a da yawa a fadin duniya.

Shugabana hukumar FBI Christopher Wray ya yabawa ‘yan sandan Dubai bisa kama Hushpuppi da Olalekan Jacob Ponle da aka fi sani da Woodberry.

Wray ya mika sakon godiyarsa ga ‘yan sandan Dubai kan namijin kokarin da suka yi na mika wa Amurka masu laifin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *