Hukumar tara kudaden haraji ta jihar Kano, ta dakatar da ma’aikatan ta 308 sakamakon karancin kudaden harajin da ake samu.

Shugaban hukumar Bala Inuwa ya bayyana haka yayin da ya ke zantawa da manema labarai, inda ya ce sun dauki matakin ne sakamakon durkushewar tattalin arziki da annobar korona ta haifar.

Ya ce an yi watsi da kamfanonin tuntuba guda 60 masu ba hukumar shawara, wadanda kwangilar su ta kare tun a shekara ta 2018 kuma su ke ci-gaba da aiki ba bisa ka’ida ba, amma kamfanonin da ke da sha’awar ci-gaba da kwangilar na iya sake shigar da bukatar hakan.

Inuwa ya kara da cewa, sun dakatar da yarjejeniyar aikin ma’aikata na wucin-gadi 308 har zuwa lokacin da kudaden shigar da jihar ke samu zai karu.

Shugaban hukumar ya cigaba da cewa, karancin kudaden gudanarwa da hukumar ke fuskanta ya kai intaha, inda gwamnatin jihar ke samun naira miliyan 500 zuwa miliyan 700 a kowanne wata, sabanin naira biliyan 2 da ta ke samu kafin bullar Korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *