Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya na da kudurin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci.

Buhari ya bayyana haka ne, a  cikin jawabin da ya aika wa Taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya a faifan bidiyo.

Akalla lissafin kididdigar Oxfam ta tabbatar da cewa, akwai ‘yan Nijeriya miliyan 94 da ba su da cin yau balle na gobe.

Shugaba Buhari, ya aika da jawabin ne a taron da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ta faya-fayen bidiyo, inda aka kafa Kungiyar Kasashen Yaki da Fatara da Talauci ta Duniya.

Kungiyar, za ta rika janyo hankalin kungiyoyin bada taimako da kasashe da sauran masu ruwa da tsaki, domin a taru a yi wa fatara da kuncin talauci dukan-kabarin-kishiya a kasashen duniya.

Da ya ke maraba da kafa wannan kungiya, Buhari ya ce tuni Nijeriya ta shiga sahun gaba wajen yaki da fatara da talauci ta hanyar kafa Shirin Inganta Rayuwa na Muradun Karni.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *