Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duk mai riƙe da muƙamin siyasa ko ma’aikacin gwamnati da aka kama yana amfani da matsayinsa wajen nemawa wasu na jikinsa aiki zai yabawa aya zakinta.

A wata sanarwa da ta fito ta bakin ministan yaɗa labarai da al’adu Lai Mohammed, shugaban ya ce hakan ya saɓa wa dokar gudanar da aikin gwamnati.

Sanarwar ta ce gargaɗin na shugaban ƙasar ya biyo bayan rahotanni da ake yawan samu kan yadda manyan ma’aikatan gwamnati da masu muƙaman siyasa da masu taimaka wa shugaban ƙasa ke amfani da katinsu ko kuma rubutacciyar wasiƙa wajen neman aiki da kuma kwangiloli.

Ministan ya ce hukumomi da ma’aikatu su yi watsi da duk wasu buƙatu da wani jami’in gwamnati ya turo musu na neman aiki ko kuma kwangila ga wani.

Ya ce gwamnati ta fitar da tsare-tsare da hanyoyin da ya kamata a bi wajen bayar da aiki ko kuma kwangila.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *