Gwamnatin tarayya ta bukaci kwamitocin da aka kafa domin daukar mutane dubu dari 7 da 74 aiki a dukkanin kananan hukumomin dake Najeriya da su ci gaba da aikinsu.

Karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi Festus Keyamo, ya bada wannan umurni a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a Abuja.

Ministan na maida martani ne kan baazanar dakatar da shirin daukar aikin da kwamitin hadakar ‘yan majalisar dokoki ya yi.

Kayemo ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari kadai ke da ikon dakatar da shirin wanda tun farko shi ya bada umurnin a fara.

Ya ce majalisar ba ta da karfin ikon ba bangaren zartaswa umurni, a cewarsa sashe na 88 na kundin tsarin mulkin 1999 ya ba ‘yan majalisar ikon gudanar da bincike ne kadai ba dakatarwa ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *