LAFTANAR JANAR TUKUR BURATAI
SHUGABAN SOJIN NAJERIYA

Babban Hafsin sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya bukaci jami’an soji dake aikin yaki da ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara su bi ‘yan ta’adda zuwa cikin dazuzzukan da suke buya.

Buratai ya bada umurnin ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ga runduna ta 2 na aikin tabbatar da tsaro dake Zurmi a jihar ta Zamfara.

Ya ce aikin yaki da ayyukan ta’addanci a yankin na da bukatar daukar salon bin ‘yan ta’addan har wuraren da suke buya a cikin dazuzzuka.

Sannan ya bukaci jami’an sojin da su ci gaba da maida hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Najeriya.

Buratai ya ba jami’an tsaron tabbacin samar musu da kayayyakin yaki na zamani ta yadda za su ci gaba da samun kwarin gwiwar tunkarar ‘yan ta’addan da suka addabi al’umma.

Buratai ya kuma kai ziyara fadar mai martaba sarkin Zurmi, Abubakar Muhammad, inda ya kara tabbatar masa cewa rundunar sojin za su kara matsa kaimi wajen yaki da ayyukan ta’addanci.

A nasa jawabin Basaraken y aba jami’an sojin tabbacin goyon baya daga al’ummar yankin a kokarin da suke na kawar da ‘yan ta’addan da suka zamawa yankin barazana.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *