Kungiyar Boko Haram ta bukaci a ba ta dala dubu ɗari biyar kwatankwacin Naira miliyan 190 kafin sakin wasu ma’aikatan agaji huɗu da wani jami’in tsaro da su ka kama.

A cikin wani hoton bidiyo da ƙungiyar ɓangaren Albarnawi ISWAP ta fitar, ta an nuna waɗanda aka kama su na rokon gwamnatin Nijeriya ta kuɓutar da su.

An kama mutanen ne tun a watan da ya gabata.

A shekara ta 2019 ma ƙungiyar ISWAP ta kashe wasu ma’aikatan agaji guda shida da ta yi garkuwa da su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *