Kwamitin masallacin ‘Yan Lilo dake Tudun Wada a Kaduna, ya mayar da limamin Masallacin da aka dakatar sakamakon saba dokokin kariya daga kamuwa da cutar korona.

Tun bayan sauke Mallam Musa daga Limancin Masallacin Juma’ar masu ruwa da tsaki suka yi ta kokarin ganin sun shiga tsakani domin dinke barakar.

Dawo da Limamin dai ya biyo bayan wani zama da aka yi tsakanin shi da Kwamitin Massallacin, a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Izala ta Jihar Kaduna, Mallam Tukur Isa.

Bayan cimma matsayar Limamin Mallam Musa ya amince zai dawo ya ci gaba da Limanci tare da bin dokokin kariya da hukumomin yaki da cutar korona suka gindaya.

Zaman sulhun wanda ya gudana a Masallacin, ya samu halartar manyan mutane, ciki harda Mai ba gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin addinai, Mallam Jamilu Albani.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *