Gwamnatin tarayya ta ce za ta sa wa wasu kananan hukumomi 18 a wasu jihohin Najeriya takunkumi.

Shugaban kwamitin yaki da cutar korona a Najeriya, kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya sanar da haka.
Ya ce kananan hukumomin sune wadanda bincike ya nuna suna dauke da kashi 60 na mutanen da suka kamu da cutar a fadin Najeriya.

Mustapha ya sanar da hakan ne jim kadan bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari kan halin da ake ciki kan kokarin dakile yaduwar cutar.

Ya ce gwamnatoci a matakan jiha da kuma kananan hukumomin da lamarin ya shafa ne za su aiwatar da matakin killace yankunan da aka fi samun masu kamuwa da cutar.

Sai dai ya ce mafi rinjayen kananan hukumomin da za a killace a jihar Legas suke, yayinda ragowar ke sauran jihohi.

Cikin kananan hukumomin har da Eti-Osa, Ikeja, Apapa, Surulere da Mushin dukkaninsu a Legas, yayinda sauran suka hada da Nasarawa a Kano, karamar hukumar Katsina a jihar Katsina, karamar Hukumar Bauchi dake jihar at Bauchi, sai kuma Dutse dake jihar Jigawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *