An yiwa wani Yaro yankan rago A Unguwar Rijiyar Lemo dake karamar hukumar Fagge a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadin da ta gabata.

Shaidun gani da ido sun ce sun jiyo yaron yana ihu na ya na neman dauki yayin da jini yake zuba ajikinsa.

Nan take al’ummar unguwar suka dauke shi zuwa asibitin Aminu Kano domin ceto rayuwarsa.

Shugaban karamar hukumar Fagge Shehu Ibrahim ya ce zai dauki nauyin jinyar yaron har ya samu lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *