Hukumomin kasar Iran Sun cafke wasu maza guda uku da suka yi yunkurin sayar da jarirai a shafin sa da zumunta na Instagram.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce, anyi nasarar ceto jariran guda biyu, daya dan kwana 20, da kuma dayan dan wata biyu.

An baje hajar jariran ne a shafin Instagram tare da bayyana farashinsu, inda aka yi wa daya kudi miliyan 400 na kasar Iran ($9,490), dayan kuma miliyan 500 kudin kasar ($11,800).

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *