An harbe wani shahararren mawaki dan kasar Habasha mai suna Hachalu Hundessa, Wanda ya yi shura a wakokin siyasa.

Kisan mawakin ya faru ne a Addis Ababa babban birnin kasar ta Habasha. Dama dai mawakin mai shekara 34 ya taba cewa an dade ana yi mishi barazanar za a kashe shi, kuma yanzu ‘yan sanda sun cafke mutane da ake zarginsu da kisan.

An samu barkewar zanga-zanga da kona-konen taya sakamakon kisan da aka yi wa mawakin, inda mutum biyu suka rasu a zanga-zangar.

Sai dai ‘yan sanda Sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye don tarwatsa taron masu zanga-zangar bisa fatgabar kar cibi ya zama kari.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *