Ma’aikatar sufurin jiragen sama da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa FAAN, sun bukaci fasin joji su kasance masu bin ka’idojin da hukumomin lafiya suka bada idan aka maido da sufurin jiragen.

Ministan kula da harkokin sufurin Sufuri Hadi Sirika, ya bayyana haka, ya ce gwamnatin tarayya ta shigo da wasu sabbin na’urorin da za su taimaka wajen takaita cudanyar jama’a.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara gwaji a kan aikin sufurin jiragen saman, yayin da ake sa ran bude filayen jiragen nan bada jimawa ba.

Hadi Sirika, ya kuma bayyana gamsuwa da wani gwajin aikin jiragen sama da su ka gudanar na na’urori da sauran kayayyakin kare kai da na yin gwajin zafin jiki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *