Gwamnan jahar Yobe Mai Mala Buni wanda shine sabon Shugaban riko na kwamitin tsara  zaben shuwabanin jam’iyar APC na kasa ya rantsar da sauran ‘yan  kwamitin za su yi aiki tare.

Jim kadan bayan rantsarwar kwamitin ya gana da tsofaffin shuwabanin jam’iyar da aka rusa a baya-bayan nan.

Gwamna Buni ya bada tabbacin cewa sabin  shugabanin jam’iyar zasu gudanar da aiki bisa gaskiya da adalci kuma  kwamitin zai gudanar da aiki cikin hazaka da kishin jam’iyyar. 

Kafin zamansa gwamnan jihar Yobe, Gwamna Buni ne tsohon sakataren  jam’iyar APC na kasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *