Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta rufe shafin yanar gizo da ta bude domin jam’iyyu su tura da sunayen ‘yan takaransu da za su fafata a zaben gwamnan jihar Edo.

Babban jami’in kula da sashen yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar Festus Okoye ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce hukumar ba ta kara wa’adin da ta bada na karfe 6 na yammacin yau Litinin 29 ga wannan watan ba.

Okoyo bai bayyana adadin jam’iyyun da suka tura da ‘yan takararsu ba, amma ya ce nan gaba kadan akwai karin bayanai da hukumar za ta fitar kamar yadda yake a doka.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *