Festus Keyamo

Gwamnatin Najeriya ta ce nan bada jimawa ba za ta fara daukar sabbin ma’aikata 774,000 a kananan hukumomi dake fadin kasar nan.

An rantsar da komitocin gudanar da aikin ne a yau 29 Yuni a duk jihohin Najeriya ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Festus Keyamo ne ya jagoranci rantsarwar da aka gudanar ta yanar gizo domin bin ka’idojin yaki da cutar korona.

A tsarin shirin za a dauki mutum 1,000 a wace karamar hukuma dake fadin kasar nan.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun ministan ya fitar a Abuja, ya ce kwamitocin  ke da alhakin zabo mutane 1,000 da suka cancanta a ko wace karamar hukuma dake Najeriya.

Ya ce a kwamitocin dake da mutane ashirin-ashirin ko wannen su na da shugaba, mataimakin shugaba da kuma sakataren.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *