Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cewa fyade aka yiwa yarinyar da aka tsinci gawarta a wani Masallaci dake Kurmin Mashi a karamar hukumar Kaduna ta kudu.

Kwamishinar kula da harkokin mata da walwalar jama’a Hafsat Baba, ta ce binciken da masana suka gudanar bayan tsintar gawar ya nuna cewa wannan ba shine karon farko da ake yiwa yarinyar fyade ba.

Ta ce jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike domin gano tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a aikata wannan mugun laifin kamar yadda doka ta tanada.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka tsinci gawar yarinyar a masallacin, wanda hakan ya ta da hankalin jama’a da dama, tare da yin kiraye-kiraye na a gudanar da bincike.

Wani Mazaunin unguwar ne ya fara ganin gawar yarinyar a harabar masallacin inda nan take ya ankarar da mutane suka taru tare da nuna damuwarsu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *