Gwamnatin tarayya ta bada damar bude makarantu ga daliban da ke shirin rubuta jarrabawar kammala makarantu da suka hada da ‘yan ajin karshe da ‘yan aji ukku 3 na sakandire sai kuma ‘yan aji 6 na Firamari.

Wannan na kunshe ne a cikin wasu sabbin ka’idoji da Kwamitin yaki da cutar korona da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa ya fitar a taron da yake gudanarwa na kwana-kwana a Abuja.

Kwamitin ya ce sabbin matakan za su fara aiki ne daga ranar daya ga watan Yuli da zamu shiga kamar yadda Shugaban kwamitin kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana.

Sauran sabbin matakan sun hada da sassauta haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi amma a iya lokutan da dokar takaita zirga-zirga ba ta aiki.

Kwamitin ya kuma umurci tasoshin mota su mallaki na’urar auna zafin jiki da kuma tabbatar da ko wanne fasinja ya sanya takunkumin rufe baki da hanci kafin ya shiga mota.

Kwamitin ya ce dokar takaita zirga-zirga a fadin Najeriya daga karfe 10 na dare zuwa 4 na safiya za ta ci gaba da kasancewa a haka.

Ya ce nan bada jimawa ba za a bada umurnin maido da hada-hadar sufurin jiragen sama na cikin gida.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *