Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya musanta rade-radin cewa an ba sanatoci gurabe a shirin N-Power da ake shirin daukar matasa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Ola Awoniyi ya fitar, Ahmed Lawan ya ce babu kanshin gaskiya a labarin.

Lawan, ya bukaci mutane su yi watsi da wadannan rahotanni da ke cewa an ba shi gurabe a aikin shirin N-Power da za a dauki matasa.

Ya ce rahotannin da wasu kafofin yada labarai ke yadawa ba wani abu ba ne illa kanzon kurege.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *