Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu

Fadar shugaban kasa ta ce ba wani takun saka da ke tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da jigo a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.

Mai taimaka wa shugaban kasa Kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce shugaba Buhari da Bola Tinubu ne su ka jagoranci kafa kafa jam’iyyar APC, kuma sun hadu ne a kan ginshikin gina kasa.

Shehu ya kara da cewa, shugaba Buhari da Tinubu sun toshe kunnuwan su daga sauraren magulmata masu kitsa makircine da hada husuma.

Ya ce su na nan tare daram kuma suna tuntubar juna akai-akai, don haka aminantakar da ke tsakanin su babu wanda zai iya shiga tsakani.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *