Tukur Buratai, Hafsan Sojin Kasa na Najeriya

Shugaban rundunar sojin Nijeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce dakarun soji za su ci gaba da jajircewa wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Buratai ya bayyana haka ne ta bakin Laftanal Janar Lamidi Adeosun yayin bikin yaye sojoji karo na 79 a Zaria.

Ya ce Nijeriya na fuskantar matsalar Boko Haram da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka.

Buratai ya ce rundunar sojin Nijeriya ta ba dakarun ta abin da ya kamata, sannan ta na sa ran za su yi iyakar kokarin su a fagen daga.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *