Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari wasu rugagen Fulani makiyaya a Osuku dake Koton Karfe a jihar Kogi, inda suka kashe mutane 2 tare da yin awon gaba da shanu dari da 3.

Basaraken gargajiyan yankin Abdulrazak Isa Koto ya tabbatarwa manema labarai cewa shugaban Fulanin yankin ya kirashi da misalign karfe 11 da rabi a daren da aka kai harin inda ya sanar masa.

Ya ce nan take aka tura jami’an tsaron sa kai suka bi ‘yan ta’addan inda suka kwato wasu daga cikin shanun.

Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro Abdulkarim Isa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an shirya jami’an tsaro da za su tafi farautar barayin tare da kwato ragowar shanun Fulanin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *