Sadiya Farouq
Ministar Jinkai ta Najeriya

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wasu wurare dakuma motocin daukar marasa lafiya biyu da za su yi aiki a matsayin cibiyar kula tare da killace masu dauke da cutar korona na sansanonin ‘yan gudun hijira dake Borno.

Mataimakiyar jami’in yada labarai a hukumar kula da harkokin jin kai Rhoda Iliya, ta tabbatar da haka, ta ce minister ma’aikatar Sadiya Farouq ne ta kaddamar da cibiyar. 

Ministar ta ce an dauki matakin hakan ne domin ba mazauna sansanonin gudun hijiran kariya ta musamman daga yaduwar cutar korona.

Baya ga haka minister ta kuma kaddamar da wasu sabbin gidaje dubu 10 da aka gida, tare da jaddada kudurin da gwamnati ke da shi na maido da zaman lafiya da ci gaba a yankin na Arewa maso gabas.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *