Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na wani babban yunkurin ganin bayan masu aikata fyade cikin gaggawa. Game da wannan lamari, abokin aikinmu Usman Kabara ya tattauna da Hafsat Mohammed Baba, Kwamishiniyar Jin Dadin Al’umma ta Jihar Kaduna
Hafsat Mohammed Baba, Kwamishiniyar Jin Dadin Al’umma ta Jihar Kaduna

Fyaden manyan mata da kanana yara ya zama ruwan dare a Najeriya, musamman arewacin kasar. Jihar Kaduna na daya daga cikin garuruwan da hakan ke faruwa, wanda hakan ce ta sa jihar zabura tare da kafa Cibiyar Kai Koken Fyade Da Cin Zarafin Saduwa. 

Kididdigar cibiyar ta nuna yadda a shekarar 2019 kadai aka sami koken fyade sau 621 a ofisoshin cibiyar guda 4 a jihar, da kuma karin koke bayan bullar cutar korona, inda aka sami koke har 485 daga Janairu zuwa Mayun shekarar 2020 a garuruwan Kafanchan da Kakuri da Zaria da Tudun Wada.

Kazantar lamarin ne yasa Gwamnan jihar Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya hada kai da masu ruwa da tsaki a jihar, ciki har da Ma’aikatar Ayyuka Da Jin Dadin Jama’a don yakar lamarin da suka kuduri aniyar ganin bayansa ko da kuwa hakan na nufin zartar da hukuncin kisa ne.

Danna sama shafin nan don sauraron hirar da muka yi da Kwamishiniyar Jin Dadin Jihar Kaduna.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *