Geoffrey Onyeama

Gwamnatin tarayya za ta maido da ‘yan Najeriya dari da 67 da suka makale a kasar Afrika ta kudu.

Ministan kula da harkokin kasashen ketare Geoffrey Onyeama, ya sanar da haka a shafinsa na twitter, ya ce akwai karin ‘yan Najeriya kashi na 2 da gwamnatin tarayya ta amince a maido dasu daga kasar Amurka.

A cewarsa jirgin na kamfanin  Air Peace dauke da mutanen ya bar filin sauka da tashin jiragen sama na O.R Tambo dake Johannesburg, na kasar Afrika ta kudu zuwa Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Ya ce za a sauke mutane 45 a babban birnin tarayya Abuja, inda daga nan kuma zai tashi zuwa filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *