Gwamnatin jihar Legas ta ce ta kulle wasu gine-gine guda 42 a Lekki domin rage yawan asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da ake samu sakamakon rugujewar gini.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun jami’in yada labarai na ma’aikatar tsara birane da karkara na jihar Mukaila Sanusi. 

Kwamishinan ma’aikatar Idris Salako, ya ce da dama daga cikin gine-ginen ba a yi su bisa ka’ida ba, kuma ba su nemi amincewar hukumomin da ya kamata ba.

Ya ce daukar irin wadannan matakai ya zama wajibi domin rage irin barnar da hakan ke haifarwa da kuma samar da tsari mai kyau wajen yin gine-gine a fadin jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *