Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce an samu karin mutane 684 da suka kamu da cutar COVID-19 a sassan kasar nan.

Humukar ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter.

Hukumar ta ce daga cikin sabbin wadanda suka kamu da cutar akwai mutane  259 a jihar Legas, 76 Rivers, 69 a Katsina, 66 a Delta, 46 a Rivers, 23 a Ogun.

Sauran jihohin da aka samu karin sun hada da Edo inda aka samu mutane 22, 21 a Ebonyi, 20 a birnin Tarayya Abuja, 16 a Kaduna, 10 a Ondo, 9 a Imo, 9 a Abia, 5 a Gombe, 4 a Plateau, 4 a Bauchi, 2 a Ekiti, 1 a Anambra.

Hukumar ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ta COVID-19 a Najeriya yanzu ya kai dubu 23 da 298, an kuma sallami mutane dubu 8 da 253 daga asibiti bayan haka mutum 554 suka mutu sakamakon cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *